Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: An gudanar da wani babban nune-nune a birnin Dar es Salaam na ƙasar Tanzania, mai taken "Daga Karbalar Sayyida Sukaina (A.S) Zuwa Karbalar Minab". Nunin ya kasance a cikin fili mai girman murabba'in mita 600, kuma an haɗa shi da wasan kwaikwayo na fage, zane-zane, da ba da labari. An raba nune-nunen zuwa sassa goma sha biyu (12) na waki’oi waɗanda suka biyo bayan lamarin Karbala tun daga lokacin Imam Hussain (A.S) har zuwa Kisan Kiyashi na Minab a Iran da kuma shahadar Jagora Shahid Ayatullah Khamene'i.
Sassan nune-nunen sun haɗa da:
1. Zaman Sukaina a kurkuku – ana nuna yadda aka zalunce ta.
2. Mafarkin yarinya – fatan rayuwa mai kyau.
3. Gidan Imam Hussain a Madina – yara suna wasa, sannan aka shirya tafiya.
4. Bankwana da Madina – Imam Hussain ya fita domin rashin yarda da wulakanci.
5. Tafiya zuwa Karbala – Zuhayr ibn Qayn ya shiga cikin mabiya Imam Hussain.
6. Jiran ruwa – yara suna jiran Abbas ya dawo da ruwa, amma bai dawo ba.
7. Runguma ta ƙarshe – Imam Hussain ya yi bankwana da 'yarsa.
8. Ali Asghar (A.S) – jariri aka kai wurin makiya don neman ruwa, amma suka kashe shi.
9. Shahadar Imam Hussain – ya faɗi a cikin masuka da kibau yana cewa "Na yarda da hukuncin Allah."
10. Kasuwar Sham – yadda aka wulakanta iyalan Imam Hussain a matsayin fursunoni.
11. Kabarin Sukaina (Ruqayya) – yarinya ta rasu saboda baƙin ciki.
12. Karbalar Minab – an nuna yadda aka zalunci mata da yara a Minab, tare da hotunan jagora shahidi Khamene'i, Sayyid Hassan Nasrallah, Janar Soleimani, da Abu Mahdi al-Muhandis.
Ƙarshen nune-nunen ya kasance mai cike da ruhaniya, inda masu kallo suka ji kamar suna tsakanin haramain (tsakanin kaburburan Abbas da Hussain). An shirya nune-nunen ne daga 2 zuwa 5 ga Yuli a Cibiyar Ayyukan Musulunci na Matasa, tare da halartar jakadan Iran a Tanzania da jami'in al'adu.
.......................
Your Comment